Home Home N-Power: Bulama Bukarti Ya Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Da Su Cigaba Da...

N-Power: Bulama Bukarti Ya Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Da Su Cigaba Da Biyan Kudaden Tallafi.

152
0
download (11)
download (11)

Wani babban lauya kuma mai sharhi kan al’umurar yau da kulum, mai suna Bulama Bukarti ya ja hankalin gwamnatin tarayya da su cigaba da biyan kudaden N-Power da ake biyan wasu matasan Najeriya #30,000 a’ duk karshen wata.

Bulama Bukarti yayi wanan jan hankalin ne a’ shafin sa na sada zumunta, inda ya ke cewa “Ina Kira ga gwamnatin tarayya da ta gagguta biyan matasan N-Power Kudaden su na tsawon watani 9 zuwa 12 da ba a’ biya ba.”
Ya cigaba da cewa “biyan wadannan matasan kudi zai basu dama su kama sana’o’I daban daban da za su iya rufa wa kansu asiri da shi ta hanyar taimakawa iyaye harda ‘yan uwa. Hakan zai kawo saukin tsananin rayuwa da ake ciki.”

Leave a Reply