Home Labarai Mutumin Da Ya Sare Kan Dan Sa Don Yayi Kudi A Jihar Delta

Mutumin Da Ya Sare Kan Dan Sa Don Yayi Kudi A Jihar Delta

30
0

Jami’an ‘yan sanda na jihar Delta, sun kama wani mutum mai suna Volt Blessing Gabriel, bisa amfani da zarto wajen sare kan dan sa mai shekara daya domin yin asirin kudi.

Gabriel wanda ya kashe dan sa mai suna Godspower a garin Benin na jihar Edo, ya binne kan mamacin ne kusa da wata bishiyar kwakwa sannan ya jefar da gawar.

Mista Gabriel, ya ce ya kashe yaron ne saboda ya yi mafarkin cewa idan ya aikata hakan, sannan ya shafe kan sa da jinin zai yi arziki.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Delta Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama Gabriel ne bayan matar shi ta gano batan dan ta sannan ta kai rahoton cewa ta na zargin mijin ta.

Da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce shi ya kashe dan sa a jejin Ewabogun, ta hanyar amfani da zarto wajen fille ma shi kai sannan ya binne shi kusa da wata bishiyar kwakwa da ke dajin ya kuma jefar da gawar yaron.