Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta NCDC ta ce mutum 167 ne suka kamu a cutar korona a ƙasar ranar Juma’a.
Haka nan, wasu mutum biyu sun rasa rayukan su sakamakon cutar.
Cikin rahoton da ta wallafa, NCDC ta ce an samu mutanen ne daga jiha 10, har da Abuja babban birnin ƙasar.
Jihohin su ne: Rivers (68), FCT (43), Lagos (24), Plateau (10), Niger (8), Edo (5), Kano (4), Benue (2), Oyo (2), Delta (1)
Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 208,797 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya. Kazalika ta kashe mutum 2,769, sai kuma 196,425 da aka sallama bayan sun warke daga cutar.