Home Labaru Mutum 80,000 Za Su Rubuta Jarrabwar Jamb Ranar 6 Ga Watan Mayu

Mutum 80,000 Za Su Rubuta Jarrabwar Jamb Ranar 6 Ga Watan Mayu

141
0

Akalla mutane dubu 80 ne za su rubuta jarrabawar JAMB da
aka sake tsara rubutawa a ranar 6 ga watan Mayu na shekara
ta 2023.

A cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar Fabian Benjamin ya fitar, ya ce an samu jinkirin ne sakamakon aikin tantance sakamakon jarrabawar da aka rubuta.

Sanarwar ta ce, ɗaliban da aka tantance a cibiyoyin rubuta jarrabawar, amma ba su rubuta jarrabawar ba, da waɗanda ba a tantance bayanan su ba da waɗanda aka samu saɓanin bayanan su za su samu saƙonnin rubuta jarrabawar.

Ta ce waɗanda su ka samu matsaloli a lokacin rubuta jarrabawar ba za su ga sakamakon su ba, maimakon haka za su samu saƙon sake rubuta jarrabawar.

Hukumar ta ce, sakamakon wani zaman gaugawa da ta yi, ta sanya ranar 6 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a sake rubuta jarrabawar ga waɗanda ba su samu rubutawa ba.

Leave a Reply