Home Labaru Mutane Takwas Sun Mutu Sakamakon Fashewar Tankar Mai A Najeriya

Mutane Takwas Sun Mutu Sakamakon Fashewar Tankar Mai A Najeriya

35
0

Akalla mutane takwas aka tabbatar sun mutu, sakamakon
fashewar wata tankar dakon mai a jihar Ondo.

Lamarin dai ya ƙazance ne yayin da wuta ta kama a daidai lokacin da mazauna garin ke dibar mai daga tankar da ta yi hatsari.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo, ta ce motar dakon man ta faɗi ne a kan titi, inda kusan duk man da ke cikin ta ya malale, inda mazauna yankin su ka mamaye wurin domin dibar mai.

Ta ce Motar ta kashe mutane takwas ta kuma raunata wasu da dama, wadanda aka garzaya da su asibiti kamar yadda kakakin ‘yan sandan ya shaida wa manema labarai.

Mazauna yankin da shaidun gani da ido sun ce, tankar ta fashe ne a wata unguwa da ke kusa da gidan mai da wani ginin coci, amma babu ko daya da gobarar ta shafa.

Leave a Reply