Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Murnar Ranar Haihuwa: Shugaba Buhari Ya Yanka Kek A Turkiyya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yanka kek ɗin murnar ranar haihuwar sa a Turkiyya bayan ya cika shekara 79 da haihuwa.

An tsara kek ɗin ne da launin Najeriya wato fari da tsanwa inda bayan ya yanka kek ɗin sai ya tattauna da hadiman sa kafin suka tafi wajen taron tattaunawa kan cinikayya tsakanin Turkiyya da ƙasashen Afrika.

Shugaban ƙasa ya bayyana cewa zai ci gaba da yin iya bakin ƙoƙarin sa wajen yi wa ƴan Najeriya aiki har zuwa lokacin da zai miƙa mulki a 2023.

Shugaban ya kuma ce zai koma gona ne domin ci gaba noma da kiwo bayan ya miƙa mulkin.

Exit mobile version