Home Labarai Muna Yi Wa Kiristocin Yankin Arewa Kaf Hudubar Kada Su Zaɓi Tinubu...

Muna Yi Wa Kiristocin Yankin Arewa Kaf Hudubar Kada Su Zaɓi Tinubu Da Shettima – Babachir

59
0

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal, ya lashi takobin ganin bayan takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima na jam’iyyar APC a zaben shekara ta 2023.

A wata hira da yayi da Talabijin na Arise, Babachir ya ce gaba ɗaya Kiristocin yankin Arewa ba za su zaɓi jam’iyyar APC a zaɓen shugaban kasa ba.

Ya ce su na bin mutanen su kiristocin yankin Arewa, inda su ke yi masu huɗubar kada su kuskura su zaɓi takarar Tinubu da Kashim Shettima.

Babachir David Lawal, ya ce tsaida musulmi shugaban kasa da mataimaki musulmi rashin adalci ne, amma shi da Yakubu Dogara da wasu gaggan kiristocin yankin Arewa su na aiki domin su karya tafiyar Tinubu da Kashim Shettima.

Idan dai ba a manta ba, tun bayan bayyana Kashim Shettima da Bola Tinubu ya yi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na na jam’iyyar APC, Yakubu Dogara da Babachir David Lawal su ka lashi takobin ganin bayan tafiyar su.