A watan da ya gabata ne a ka kama shugaban kamfanin
Binance, Tigran Gambaryan tare da abokin aikinsa, Nadeem
Anjarwalla, wanda ke da fasfon Birtaniya da Kenya a wani
ɓangare na binciken kaucewa biyan haraji da gwamnatin
Nijeriya ke yi wa kamfanin na kuɗin kirifto.
Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya shaida cewa, a duk lokacin da a ka samu wata matsala ta tsare ɗan ƙasarsu a wata ƙasa, to ofishin jakadancin da ke ƙasar na yin duk mai yiwuwa wajen bayar da taimakon da ya dace.
Ofishin jakadancin ya ƙi bayar da cikakken bayanai game da tsare ɗanƙasar, yana mai cewa ya yi hakan ne saboda wasu dalilai na sirri.
A halin yanzu, Nadeem Anjarwalla ba ya hannun jami’an Nijeriya bayan da mahukuntan ƙasar su ka tabbatar da cewa ya tsere, sai dai wata majiya daga makusantansa ta ce ya bar Nijeriya ne ta hanyar da ta dace. Mahukuntan Nijeriya na aiki da jami’an tsaro don samar da takardar sammaci ga Anjarwalla.