Kungiyar Manyan dillalan Mai masu zaman kan su ta IPMAN, ta ce ta na maraba da shirin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya za ta yi a shekara ta 2022.
Shugaban kungiyar Chinedu Okoronkwo ya bayyana wa manema labarai haka a Legas, inda ya tun ranar 16 ga watan Agusta na shekara ta 2021, Shugaba Buhari ya soke tallafin mai tun da ya sa hannu a kan sabuwar dokar PIA.
Ya ce a matsayin su na ‘yan kasuwa, mun dade su na ba Gwamnati shawarar a cire tallafin mai, domin babu amfani ko wani ci-gaba.
Chinedu Okoronkwo, ya ce abin da su ke so shi ne, a yi daidaito wajen ba kowa ‘yancin saida hajar sa yadda ya ke so bayan an cire tallafin.