Home Labarai Muna Ci Gaba Da Buga Sabbin Kudi Yanzu -Cbn

Muna Ci Gaba Da Buga Sabbin Kudi Yanzu -Cbn

92
0

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya ce ya na ci-gaba da buga
sababbin takarkun kudi, sai dai har yanzu ‘yan Nijeriya na
kuka da cewa su na ci-gaba da fuskantar matsala wajen samun
takardun kudi.

Lamarin dai ya sake kunno kai ne, a daidai lokacin da wasu ‘yan Nijeriya ke ci-gaba da yin korafi game da yadda ba su iya samun adadin takardun kudin da su ke bukata a bankunan kasuwanci baya ga matsalar na’ura da sabis mai inganci wajen tura ko karbar kudi ta Intanet ko manhajojin bankunan da ake fama da su.

Darakta mai kula da harkokin bankuna na bankin CBN Malam Haruna Bala Mustapha, ya ce bankin ya na ci-gaba da buga sabbin takardun kudi tare da rarraba tsoffi don a samu wadata a kasar nan.

Ya ce wasu ‘yan Nijeriya idan su ka samu sabbin tsakardun kudi su na ajiyewa ne don gudun abin da ka je ya dawo nan gaba, amma nan ba da jimawa ba za a samu saukin al’amarin sossai.

Leave a Reply