Home Labaru Muna Ƙoƙarin Tabbatar Da Tsaro Kafin Rantsar Da Sabuwar Gwamnati – Usman...

Muna Ƙoƙarin Tabbatar Da Tsaro Kafin Rantsar Da Sabuwar Gwamnati – Usman Baba

85
0

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba,
ya ce su na iyakar ƙoƙarin su domin tabbatar da tsaro da ganin
an yi bikin rantsar da sabon shugaban ƙasa Bola Tinubu ba
tare da tangarɗa ba.

Usman Alkali Baba, ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa an kare martabar dimokuraɗiya a Nijeriya.

Shugaban ‘yan sandan, ya kuma gargaɗi ƴan siyasar da ke yunƙurin haifar da yamutsi ko tunzura mutane su yi hattara, tare da nesanta kan su daga duk wani abu da zai zama matsala a lokacin rantsuwar.

Usman Alkali Baba ya ƙara da cewa, ya na fatan kowa zai mutunta ‘yancin demokuraɗiyya domin ganin an kare martabar Nijeriya a idon duniya.

Leave a Reply