Gerard Pique ya samu jan kati a wasansa na karshe gabanin yin murabus inda Barcelona suka taso daga baya suka doke Osasuna da ci 2-1 a gasar La Ligar Spain, lamarin da ya kai su saman teburin gasar da tazarar maki 5 tsakanin su da Real Madrid da ke matsayi na 2.
Gerard Pique, mai shekaru 35 ya samu jan kati ne duk kuwa da cewa yana kan benci bayan da ya nuna wa alkalin wasa rashin da’a.
Ya fusata ne saboda matakin alkalin wasan na ba Robert Lewandowsky katin gargadi na biyu a minti na 31 da fara wasa.
David Garcia ne ya ci wa Osasuna kwallon ta daya tilo a wasan, kafin Pedri da Raphinha su ci wa Barcelona kwallaye 2.
Wannan ne karo na 2 kawai da aka kori Lewandowski daga wasa tun da ya fara sana’ar kwallon kafa.
Barcelona sun yi amfani da damar da suka samu ta rashin nasarar da Madrid suka yi, inda suka rike wuta har suka yi nasara a wannan wasa.