Home Labaru Mulkin Nijeriya Da Wuya – Buhari

Mulkin Nijeriya Da Wuya – Buhari

1130
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya ce akwai wahala kwarai wajen gabatar da nasarorin gwamnatin sa ga ‘yan Najeriya, inda ya dora laifin a kan manyan ‘yan Nijeriya da ke sa ra’ayin kan su a ciki.

Buhari ya bayyana haka ne, a lokacin da ‘yan kungiyar magoya bayan shi su ka ziyarce shi a fadar sa da ke Abuja.

Ya ce ba karamin aiki ba ne gabatar da nasarorin gwamnatin sa, amman dole su yi abubawan da su ka dace tunda sun sha alwashin kawo canji.

Shugaba Buhari ya cigaba da cewa, ya zama wajibi su kai Nijeriya zuwa mataki na gaba, tare da bada tabbacin cewa Nijeriya za ta gyaru fiye da yadda suka same ta.

Leave a Reply