Kungiyar dattawan Arewa, ta buƙaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zaɓe a kan maganar tsaro da kawar da fatara.
Ta ce Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya wasu muhimman alƙawurra, wanda ta ke fatan cewa zai mutunta su.
A cikin wata sanarwar taya murna ga shugaba Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima, Ƙungiyar ta tunatar da su irin rantsuwar da su ka yi, wadda ya kamata ta zamto jagora a gare su har zuwa ƙarshen mulkin su.
Kungiyar, ta ce za ta yi aiki tare da Shugaba Tinubu da gwamnoni domin tabbatar da ganin an cika alƙawurran da su ka yi wa ‘yan Nijeriya game da tsaro da inganta tattalin arziki domin rage talauci da fargaba.