Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Mufti Isma’il Menk, ya ce daliban jami’ar Al-Qalam da ke jihar Katsina sun ba shi kunya matuka game da tarbiyar su.
Malamin ya bayyana haka ne, yayin da ya gabatar da jawabi da nasihohi a makarantar, kamar yadda ya saba gabatar da karatu a makarantu da dama a fadin duniya.
Mufti Menk, ya ce dabi’ar daliban ta ba shi mamaki mutuka, ta yadda su ka rika yin surutu a daidai lokacin da ya ke gabatar da jawabi. Yayin da ya zanta da manema labarai, wani dalibin makarantar ya ce, Malamin ya fara gabatar da jawabi ne a daidai lokacin da surutun daliban yayi yawa, lamarin da ya sa dole ya dakatar da jawabin ya fice.