Home Labaru Mu Na Son Sanin Matsayar Tinubu Kan Yaki Da Cin Hanci –...

Mu Na Son Sanin Matsayar Tinubu Kan Yaki Da Cin Hanci – Kungiyoyin Fararen Hula

100
0

Kungiyoyin fararen hula sama da 30 da ke fafutukar kare
fararren hula da sa-ido a kan harkokin yaki da cin hanci da
rashawa, sun ce kamata ya yi shugaba Tinubu ya fito kararra
ya bayyana matsayin sa game da mahimmancin yaki da cin
hanci da rashawa a Nijeriya.

Jagoran kungiyoyin Auwal Musa Rafsanjani ya bayyana matsayar da su ka dauka ta yin kiran, a kan bukatar shugaba Tinubu ya fito kai tsaye ya bayyana matsayin sa game da batun yaki da almundahana a Nijeriya.

Fitaccen masanin kundin tsarin mulki a Nijeriya Barista Mainasara Kogo, ya ce tsarin mulki ya wajabta wa duk wani jami’in gwamnati ya yaki cin hanci da rashawa.

A cikin shawarwarin da su ka ba gwamnatin Tinubu, kungiyoyin sun bukaci a kaddamar da dokar kariya ga jami’an EFCC da ICPC da saura cibiyoyin yaki da almundahana, a kuma kare masu kwarmata bayanai a Nijeriya.

Leave a Reply