Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris Malagi, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su haɗa kai domin inganta al’amurran ƙasar nan.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar yaɗa labarai Malam Suleiman Haruna ya fitar, ta ce ministan ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya ta kai masa, inda ya ce aikin sa daga shugaban ƙasa Bola Tinubu shi ne bada fifiko da sake fasalin kasa domin inganta zaman lafiya da haɗin kai da ci-gaban al’umma.
Ya ce dole ne ‘yan Nijeriya su haɗu su kasance masu gaskiya da riƙon amana, su kuma tabbatar da cewa duk abin da ke damun su an gyara shi.
Mohammed Idris, ya bukaci ‘yan cibiyar su haɗa kai da shi wajen gudanar da wannan aiki, inda ya jaddada muhimmancin gaskiya da riƙon amana wajen gyara duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga ci-gaban ƙasa.
You must log in to post a comment.