Home Labarai Miyagun Kwayoyi: NDLEA Ta Kama Wani Da Take Zargi Babban Dilan Ne

Miyagun Kwayoyi: NDLEA Ta Kama Wani Da Take Zargi Babban Dilan Ne

23
0

Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta sun kama mutumin da hukumar ke nema ruwa-a-jallo.

A wasu jerin saƙonni da hukumar ta wallafa a shafin ta na Tuwita, hukumar ta ce ta ƙwace tan 7.7 na tabar wiwi, da ƙwayoyin Tramadol da yawan su ya kai 497,900 tare da kama mutum 20 da ake zargi da safarar muggan ƙwayoyin a samamen da jami’an hukumar suka ƙaddamar a jihohin Ogun da Osun da Ondo da kuma jihar Edo.

Hukumar ta ce kwana 10 bayan da ta ayyana neman sa ruwa-a-jallo, jami’an ta sun kama Ademola Afolabi Kazeem wanda suke zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.