Wasu da ake zargin fusatattun masu faskwaurin shinkafa ne sun kai hari kan jami’an Hukumar Kwastam da ke aiki a shiyyar Yauri ta Jihar Kebbi.
Wannan na ƙunshe cikin wata takarda da kakakin Kwastam shiyyar Yauri, Mohammed Tajudeen Salisu ya aika wa shugaban hukumar a Jihar, Iheanacho Ernest Ojike.
Ya bayyana cewa wasu da ake zargin fusatattun masu shigo da shinkafa ta barauniyar hanya sun kai hari ofishinsu da ke Yauri, inda suka ƙwaci bindiga kirar AK47 guda ɗaya, da buhunan shinkafa 29 daga cikin buhuna 41 da hukumar ta kwace.
Sai dai Salisu ya bayyana cewa bayan artabu da aka yi tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar ƙwato bindigar da maharan suka kwace, amma fa dai shinkafa ta tafi.