Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or da ake ba gwarzon dan wasan kwallon kafa da ya fi nuna bajinta a shekara, inda ya doke abokan takarar sa Robert Lewandowski da Karim Banzema wajen lashe kyautar.
A karo na bakwai kenan da Messi ke lashe Ballon d’Or, yayin da yake ganin cewa, nasarar lashe wa kasar sa ta Argentina gasar kofin Kudancin Amurka, ita ce, ta sanya aka mika masa kyautar a bana.
Masana harkar tamola a duniya sun bayyana cewa, babu wanda ya cancaci lashe Ballon d’Or a bara sama da Lewandowski, na Bayern Munich amma aka soke bikin bada ita saboda annobar Korona.
A bana dai, Lewandowski ne ya zo na biyu a jerin wadanda suka fi iya taka leda, sai Jorginho na Chelsea da ya yi na uku, yayin da Benzema na Real Madrid ya yi na hudu.
‘Yan jarida 180 ne daga sassan duniya ke zaman tantance dan wasan da ya cancaci lashe kyautar ta Ballon d’Or a duk shekara.
A bangaren mata kuwa, yar wasan Barcelona Alexia Putellas ce ta lashe kyautar ta Ballon d’Or a wannan shekara ta 2021.

