Home Labarai Mayakan ISWAP Sun Kashe Mutane 30 A Kauyen Dikwa A Jihar Borno

Mayakan ISWAP Sun Kashe Mutane 30 A Kauyen Dikwa A Jihar Borno

224
0

Mayakan kungiyar ISWAP, sun kashe akalla mutane 30 a matsayin ramuwar gayyar kisan kwamandan su da sojoji su ka yi ta hanyar kai harin sama a Jihar Borno.

Majiyoyi daga yankin sun shaida wa manema labarai cewa, mayakan sun kai hari ne a kauyen Mudu da ke Yankin Dikwa.

Wani shugaban ‘yan Sa-kai Babakura Kolo da ke Maiduguri, ya ce mayakan sun yanka akasarin mutanen da su ka kama ne, wadanda maza ne da ke kokarin tserewa daga yankin.

Ya ce akasarin wadanda aka kashe ’yan gwangwan ne da ke neman karafa daga motocin da aka kona ko aka daina amfani da su a yankin.

Wani shugaban ‘yan Sa Kan Umar Ari, yace mayakan ISWAP sun zargi wadanda su ka kashe ne da ba jami’an tsaro bayanai game da harkokin su.

Leave a Reply