Home Labaru Matsin Tattalin Arziki: Nijeriya Na Iya Komawa Ruwa Tsundum – CBN

Matsin Tattalin Arziki: Nijeriya Na Iya Komawa Ruwa Tsundum – CBN

380
0

Gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele, ya bayyana tsoro a kan yiwuwar Nijeriya ta kara komawa cikin matsin tattalin arziki, matukar ba a dauki matakan shawo kan matsalar rashin aikin yi da wasu rigingimu da ke damun tattalin arziki ba.

Emefiele ya bayyana haka ne, yayin gabatar da jawabi a wajen bikin yaye dalibai a jami’ar Benin da aka yi ranar Larabar da ta gabata.

A cewar sa, dole hukumomi su fara tunanin bullo da tsare-tsaren da za su kawo karshen kalubalen da tattalin arzikin Nijeriya ke fuskanta.

Ya ce ya na shakku a kan rashin tabbas ta fuskar tattalin arziki, domin tattalin arzikin duniya ya na fuskantar kalubalen da ko ana so ko ba a so zai iya haifar da matsin tattalin arziki a Nijeriya.

Godwin Emefeile ya kuma bada tabbacin cewa, babban bankin Nijeriya zai cigaba da daukar matakan da za su rage radadin matsin tattalin arziki, musamman wadanda kan iya samun tushe daga kasashen ketare.

Leave a Reply