Kungiyar masu manyan motocin dakon kaya ta Najeriya, wato NARTO, ta ce daga yanzu ba za ta sake zuba ido tana bari mutane suna tare motoci dauke da kaya suna daka musu wawa ba.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata hira da shugaban ta Alhaji Yusuf Othman, inda yake kokawa a kan yadda ake samun karuwa a hare-haren da ake kai wa manyan motoci da ke dauke da abinci a wasu jihohi.
Kungiyar ta ce matsalar ta kai matakin da ba za ta zauna tana gani ana sace musu kayan da suke dako ba da sunan wai na gwamnati ne.
Shugaban kungiyar ya ce, kayan da suke dauka ba na gwamnati ba ne kamar yadda wasu jama’a ke fakewa da haka suna tare motocin su a sassa daban-daban na kasa suna daka musu wawa wai saboda tsananin rayuwa da ake ciki.
Kungiyar ta ce suna nan suna tattaunawa da duk wadanda ya kamata domin daukar mataki kan yadda za su bullo wa lamarin domin a cewar ta ba zai yiwu mutanen ta suna aiki ana fada musu suna yin asara ba.