Home Labaru Matsin Lamba: Manyan Alƙalai Sun Buƙaci Birtaniya Ta Daina Siyar Wa Isra’Ila...

Matsin Lamba: Manyan Alƙalai Sun Buƙaci Birtaniya Ta Daina Siyar Wa Isra’Ila Makamai

58
0

Tsofaffin alƙalan kotun ƙoli sun bi sawun masana shari’a fiye da 600 wajen kira ga gwamnatin Birtaniya ta daina sayar wa Isra’ila makamai.

Cikin wata takarda da suka rubuta zuwa ga firaiminista Rishi Sunak, tsofaffin alƙalan sun ce dole ne a kawo ƙarshen fitar da makamai saboda Birtaniya na cikin haɗarin karya dokokin duniya.

Tsohuwar shugabar kotun ƙoli, Lady Hale na cikin masana sama da 600 da suka sa hannu kan takardar mai shafuka 17.

Takardar ta ce akwai buƙatar a ɗauki mataki na gaske domin hana Birtaniya faɗawa matsalar karya dokokin ƙasa da ƙasa har da yiwuwar saɓa yarjejeniyar da ta shafi dokokin kisan kiyashi.

Sauran mutanen da suka sa hannu kan takardar sun haɗa da tsofaffin alƙalan kotun ƙoli Lord Sumption da Lord Wilson tare da wasu alƙalai tara da manyan lauyoyi 69.

Tuni dai Firaminista Rishi Sunak yake fuskantar matsin lamba bayan sojojin Isra’ila sun kashe wasu ma’aikatan agaji bakwai.

A ranar Talata ne, firaiministan ya ce Birtaniya tana da wani tsari na kaffa-kaffa game da lasisin makamai.

Leave a Reply