Home Labaru Matsalar Zamfara: ‘Yan Najeriya Ba Su Yi Min Adalci Ba – Buhari

Matsalar Zamfara: ‘Yan Najeriya Ba Su Yi Min Adalci Ba – Buhari

235
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tsokaci a kan kashe-kashen da ake fama da su a jihar Zamfara, inda ya maida martani ga masu zangar-zangar yin Allah-wadai da lamarin.

Buhari ya ce kare dukiyoyi da rayukan ‘yan Npjeriya ne abin da ya sa gaba a ko da yaushe, don haka rashin adalci ne a ce bai damu da abin da ya ke faruwa a Zamfara ba.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yankin Gabas Ta Tsakiya, yayin da ya ke amsa gayyatar wasu sarakunan Larabawa domin shiga taron tattalin arziki na duniya.

Ya ce shirme ne da rashin adalci a ce bai damu da abin da ya ke faruwa a Jihar Zamfara ba.

Shugaba Buhari, ya ce a shirye su ke su kawo karshen wadannan miyagun ‘yan bindiga, don haka sun tura jami’an tsaro zuwa lungu da sako inda abin ke faruwa kuma su na kara azama.

Buhari ya kara da cewa, ya na tabbatar da cewa za su cigaba da yin iyakar kokarin su don karfafa wa jam’ian tsaro gwiwa su tunkari lamarin da karfin da ya dace.