Home Labaru Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Achaba Biyu A Kaduna

Matsalar Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Achaba Biyu A Kaduna

428
0

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun kashe wasu ‘yan achaba biyu a wani gidan mai da ke Kaduna.

Maharan, sun yi wa ‘yan achabar kisan wulakanci a gidan man Usmania da ke kan titin Nnamdi Azikwe a Kaduna.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe hudu saura kwata daren Lahadin da ta gabata, yayin da ‘yan fashin su ka kai mamaya a gidan man, inda a nan ne ‘yan acabar su ke kwana.

‘Yan fashin sun yi wa mutanen fashin wayoyi da kudade kafin su kashe su.

Daya daga cikin mutanen da ya tsira da ran sa Rayyanu Yahaya Dawakin Tofa, ya ce ‘yan fashin sun sace masa wayoyi da kudade.

Mamallakin gidan man Alhaji Abubakar Usman Sharif, ya ce an sanar da lamarin ga hukumar tsaro.

Da aka tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo, wanda ke a cikin wata ganawa ya ce za a ji daga gare shi.

Leave a Reply