Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari Ya Gana Da Sarakunan Kudu Maso Yammacin Nijeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da sarakunan gargajiya daga yankin kudu maso gabashin Nijeriya a fadar sa da ke Abuja.

Ganawar, wadda ta gudana da misalin karfe 12:30 na rana, ta samu halartar  Sarkin Ife, da Oba Adeyeye Ogunwusi.

Idan dai za a iya tunawa, Oba Adeyeye Ogunwusi ya kai wa shugaba Buhari ziyarar ban-girma makamanciyar wannan a ranar 18 ga watan Yuli a madadin sauran sarakunan gargajiya na kudu maso yammacin Nijeriya.

Yayin ganawar, Sarkin ya gabatar da matsalar tabarbarewar tsaro a yankin kudu maso gabas a gaban Shugaba Buhari, inda ya yi gargadin cewa yankin su ba ya fatan duk wani mataki na yaki.

Exit mobile version