Home Labaru Matsalar Tsaro: Sarkin Katsina Ya Ba Ministoci Sako Zuwa Ga Shugaba Buhari

Matsalar Tsaro: Sarkin Katsina Ya Ba Ministoci Sako Zuwa Ga Shugaba Buhari

366
0

Mai martaba Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman, ya bukaci ministan noma Audu Ogbeh ya sanar da shugaba Muhammadu Buhari cewa manoma da makiyaya a jihar Katsina sun bar gonakin su da dabbobin su saboda tsoron masu garkuwa da mutane.

Ministan da gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele sun ziyarci fadar Sarkin Katsina, inda su ka je domin gabatar da Irin Auduga da kayan noma ga manoman jihar Katsina.

Sarkin Katsina ya ce, ya na so a sanar da shugaba Buhari cewa ya kamata ya lura da jama’a, sannan a kare lafiyar mutane, domin duk wadannan shirye-shiryen da ake kaiwa ba za su taba aiki ba har sai an tabbatar da cewa an magance tsaro a Nijeriya.

Ya ce a kullum sai ya samu rahoto daga Hakimai da masu gari da ke nuna cewa an sace mutane ko an kashe, inda ya zargi wasu manyan kasa da ‘yan siyasa da hannu a cikin kashe-kashen da ke faruwa a Nijeriya.