Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ja hankalin ‘yan Nijeriya cewa kada su siyasantar da rikicin da ya addabi jihar Zamfara.
Wasu manyan malaman addinin Musulunci, sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa su kawo karshen kisan gillar da ake yi wa jama’a a sassa da dama na Nijeriya.
A ranar Juma’ar da ta gabata, malamai da dama sun yi hudubar musamman dangane da abin da ya ke faruwa da kuma neman gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara su dauki mataki.
Babban malami Dakta Sani Umar Rijiyar Lemo, ya ce su na kira ga mahukunta su tashi tsaye domin kare jama’a da samar masu zaman lafiya domin hakkin mutane ne a kan su kuma sai Allah Ya tambaye su.
Kamar yadda shehin malamin ya bayyana a shirin Fatawar da ya ke yi a gidan talbijin da rediyo na Rahama, ya ce duk wanda ke da hakkin yin wani abu, to sai Allah Ya tsare shi a ranar kiyama domin ya bada bahasi.
You must log in to post a comment.