Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Matsalar Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Ce Aikin Manyan Hafsoshin Tsaro Na Kyau

Majalisar dattawa ta nuna gamsuwarta a kan yadda manyan shugabanin hukumomin tsaro ke tafiyar da ayyukan samar da tsaro a faɗin Nijeriya.

Bayanin haka na zuwa bayan shafe sa’o’i 10 ‘yan majalisar na taron sirri tare da manyan hafsoshin tsaro da wasu fitattun ministoci a ranar Talata.

Yanzu haka dai, majalisar dattawa ta ce ta gamsu da irin haɓɓasan da shugabannin tsaron ke yi wajen daƙile matsaloli da ƙalubalen tsaro a Nijeriya.

Majalisar ta kuma bukaci shugabannin tsaron su kara zage damtse wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.

Da ya ke tabbatarwa manema labarai bayanan da aka cimma a taron, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya ce manyan hafsoshin tsaro mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro sun amsa tambayoyin da suka jiɓinci matsalolin tsaron Nijeriya.

Akpabio ya ce amsoshin da suka ba da sun gamsar da majalisar, musamman yadda suka karin haske a kan irin ayyukan da jami’an tsaro ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da daƙile ta’addanci a faɗin Nijeriya.

Exit mobile version