Home Home Matsalar Tsaro: Mabiya Darikar Kadiriyya Sun Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman

Matsalar Tsaro: Mabiya Darikar Kadiriyya Sun Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman

128
0
Mabiya Darikar Kadiriyya a Najeriya sun gudanar da addu’o’i na musamman domin neman dauki daga Allah Ya kawo karshen mastalar tsaro da ta addabi Najeriya, musamman yankin Arewa.

Mabiya Darikar Kadiriyya a Najeriya sun gudanar da addu’o’i na musamman domin neman dauki daga Allah Ya kawo karshen mastalar tsaro da ta addabi Najeriya, musamman yankin Arewa.

Da yake jagorantar taron addu’o’in, Shugaban Darikar Kadiriyya na Afirka ta Yama, Sheikh Muhammad Karibullah Nasiru Kabara, ya ce gudanar da irin addu’o’in a duk lokacin da wani bala’i ya samu mutane, koyarwa ce ta Annabi Muhammad (SAW).

Malamain ya ce idan muka yawaita addu’o’i, Allah zai amsa rokon mu kuma in Allah Ya yarda Allah zai fitar da mu daga wannan hali da muke ciki, saboda haka yin shi abu ne mai muhimmanci idan aka shiga cikin tsanani.

Shugaban na Kadiriyya ya kuma bayyana cewa gudanar da addu’ar ta zama dole duba da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya da sauran sassan duniya, wanda abin damuwa ne.

Leave a Reply