Home Labaru Matsalar Tsaro: Frank Mba Ya Warware Aya Da Tsakuwa

Matsalar Tsaro: Frank Mba Ya Warware Aya Da Tsakuwa

378
0
Frank Mba, Mai Magana Da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda
Frank Mba, Mai Magana Da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya bayyana dalilan da ya sa har yanzu aka gaza shawo kan matsalar garkuwa da mutane a Najeriya.
Frank Mba ya ce akwai matsaloli da ke adabar al’umma da suka hada da rashin ayyukan yi da matsanancin talauci da shan miyagun kwayoyi da sauran su.
Ya ce hanyoyin da za a bi domin magance wannan matsalar sun hada da kaddamar da shirin samar da aiki ga dimbin matasa a Najeriya, musamman harkar wasanni da motsa jiki da harkar noma da kasuwanci.
Mba, ya ce cikin masu garkuwa da mutane 261 da aka kama a Najeriya, 131 cikinsu an kama su ne cikin watanni uku bayan kaddamar da atisayen ‘Operation Puff Adder’.