Rahotanni daga yankin jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar, sun tabbatar da cewa wasu da ake zaton ‘yan Boko Haram ne, sun yi awon gaba da wasu mutane 13.
Wannan lamari dai ya faru ne a garin Timur wanda ke da nisan kilomita 60 daga garin Diffa.
Wani ganau ya ce, a daren Laraba ne wasu da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram suka shiga garin na Timur inda suka yi awon gaba da mutane 13.
Ya ce, daga cikin mutanen da aka sacen akwai matan aure uku da kuma wani malami wanda aka kashe.
Ya ce duk da jami’an tsaro na iya bakin bakin kokarinsu, akwai matsalar tsaro a yankinsu.
Mahukunta a kasar dai ba su ce komai ba a game da sace mutanen.
Ana dai yawan samun kai hare-hare a wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar, wanda kuma ya ke sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.
Ko a kwanakin baya ma kungiyar IS ta yi ikirarin daukar alhakin mummunan harin da ya yi sanadin mutuwar a kalla sojojin Nijar 29 a kusa da kan iyakar Mali.