Home Labaru Matsalar Rashin Tsaro: Ndume Ya Shawarci Shugaban Kasa Buhari

Matsalar Rashin Tsaro: Ndume Ya Shawarci Shugaban Kasa Buhari

361
0

Dan takarar kujerar shugaban majalisar dattawa, Sanata Muhammadu Ali Ndume, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da komai a halin yanzu, ya mayar da hankali ga bangaren  tsaro a Najeriya.

Sanata Ndume, ya yi korafin cewa kusan kowani yanki na Najeriya na fuskntar kalubalen tsaro wanda ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki mataki.

Ndume,  ya nuna bacin rai game da yadda kungiyar Boko Haram ke kara kaimi wajenkai hare-haren ta’addanci, inda ya roki gwamnati da hukumomin tsaro su magance matsalar.

Ya ce sun gaji da jin zancen an magance matsalar ‘hare-haren Boko Haram’ ko kuma an gama da Boko Haram, saboda ya kamata tuntuni a gama  su.

Muhammadu Ali Ndume, ya bayyana goyon baya akan kafa yan sandan jihohi domin magance rashin tsaro, ya bada shawara ga kowace jiha dake da niyyar yin hakan, su yi koyi da kasashe dake gudanar da irin tsarin aikin ‘yan sanda.