Home Labaru Matsalar Lantarki: Biyan Kudi Ne Kawai Zai Kawo Dai-Da-Ito-Akinwumi Adesina

Matsalar Lantarki: Biyan Kudi Ne Kawai Zai Kawo Dai-Da-Ito-Akinwumi Adesina

222
0

Shugaban bankin raya nahiyar Afirka Akinwumi Adesina ya ce sai Nijeriya ta samar da kwararan dabaru na biyan kudin wutar lantaki kafin ta iya magance karancin wutar da ya addabe ta.

Adesina ya sanar da hakan ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jin kadan bayan kammala ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar sa, bangaran wutar lantarki na da gagarumar rawar da ya ke takawa ga masana’antun ganin cewa, Nijeriya itace kasar da ta fi kowace kasa a nahiyar Afrika karfin tattalin arziki, inda ya yi nuni da cewa, za’a iya yin amfani da wutar wajen gudanar da abubuwa da dama.

Shugaban bankin ya kara da cewa, daya daga cikin dabarun da gwamnatin tarayya ya kamata ta yi shine, samar da kyakyawan tsarin biyan kudin lantaki domin rashin yin hakan zai yi wuya a samu masu zuba jari, musamman a fannin makamashi da kuma shawo kan matsalar durkushewar wutar.