Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Matsalar Fyade: ‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi A Katsina.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama wasu mutun biyu da ta jima tana nema kan zargin su da yi wa wata matar aure fyade, suka kuma kashe ta.

Lamarin dai ya faru ne a watan Mayu a wani kauye da ke karamar hukumar Bakori ta jihar.

Rundunar ta bayyana damke mutanen ne kwana daya bayanwata nasarar da ta ce ta yi kuma ta kama wani mutum mai shekara 51 da ake zargi da lalata kananan yara mata ciki har da mai shekara hudu.

Kakakin rundunar ‘yansandan ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya Shaidawa manema labarai cewa za su ci gaba da aiki tukuru domin ganin an kawo karshen aikata miyagun laifuka a jihar. A cikin ‘yan watannin nan an samu karuwar masu aikata fyade da lalata kananan yara musanman a yankin arewacin kasar nan.

Exit mobile version