Home Labaru Kiwon Lafiya Matsalar Fyaɗe: Ana Bincike Kan Mutumin Da Ya Yi Wa Ƴar Shekara...

Matsalar Fyaɗe: Ana Bincike Kan Mutumin Da Ya Yi Wa Ƴar Shekara Huɗu Fyaɗe A Masallaci A Bauchi

711
0

Rundunar ‘yan sanda a garin Bauchi ta ce tana ci gaba da bincike kan wani mutum mai shekara 50, da aka kama ana zargin ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara hudu fyade a cikin masallaci.

Bayanai na nuni da cewa jama’ar gari ne suka fara kama mutumin a masallaci tare da yarinyar, inda suka lakaɗa masa duka kafin daga bisani ‘yan sanda suka shiga cikin lamarin.

A cikin ‘yan watannin nan dai ana samun yawaitar rahotannin fyade a Najeriya.

DSP Ahmad Muhammad Wakil ya ce tun ranar Alhamis ne suka kwaci mutumin daga hannun jama’a, suka kuma kai shi a ka yi masa magani a asibiti.

DSP Ahmad ya ce a shekarun 2001 da kuma 2015 mutumin ya yi zaman gidan kaso na shekaru saboda kama shi da laifin fyade, kafin gwamnati ta yi masa afuwa.

Rundunar ƴan sandan na fata a wannan karon za a daukar wa mutumin mataki mai tsanani, ba a jima ba da gwamnatin jihar Bauchi ta kafa wata doka mai yaki da irin wadannan dabi’u, da ta kuma tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa yara kanana Fyaɗe.

Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, kuma ya ce matsalar gagaruma ce.

Leave a Reply