Home Labaru Ilimi Matawalle Ya Rufe Wata Makaranta Saboda Wulakanta Al-Kur’ani A Zamfara

Matawalle Ya Rufe Wata Makaranta Saboda Wulakanta Al-Kur’ani A Zamfara

678
0
Mohammed Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara
Mohammed Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle ya bada umarnin rufe wata makarantar firamare a jihar sakamakon yadda ake wulakanta Al-Kur’ani.

A wata sanarwa da daraktan yada labaran gwamnatin jihar ya fitar, ya ce gwamnan ya bada umarnin rufe Shattima Model Primary School da kuma dakatar da malaman ta.

Haka huma ya kuma umarci hukumar kula da ilimi a matakin farko ta jihar da kara daukar masu gadi domin kai su makarantun firamare da ke fadin jihar Zamfara domin tsaurara tsaro.

Gwamnan ya kuma ba jami’an tsaron jihar da kuma hukumomin da ke aiwatar da harkokin Shari’a umarnin kafa kwamiti, domin gudanar da bincike a kan yadda ake wulakanta Al-Kur’ani mai girma a jihar.

Gwamnan ya sha alwashin daukar tsatsauran mataki ga duk wanda aka samu da hannu wajen wulakanta Al-Kur’ani, sannan ya yi kira ga manyan malaman jihar da ma Nijeriya baki daya su ja hankalin al’umma ta hanyar yi masu wa’azi a kan irin munanan dabi’ur da su ke aikatawa.