Fiye da y’ay’an jam’iyyar APC dubu 12 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, kuma suka samu kyakkyawar tarba daga gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle.
Gwamnan ya karbi ‘ya’yan jam’iyyar APC ne a ranar a garin Gusau, kuma daga cikin su akwai tsofaffin kwamishinoni guda uku da suka hada da Alhaji Idris Keta, Alhaji Abdulkadir Ahmed da Alhaji Aliyu Tsafe.
Sauran sun hada da tsofaffin shuwagabannin kananan hukumomi da suka hada da Alhaji Musa Tsafe, da Alhaji Ahmed Kantoma, da wasu tsofaffin manyan daraktoci.
Da suke gabatar da jawaban su, daban daban Idris Keta da Habibu Alo, sun bayyana cewa abin da ya ja hankalinsu zuwa jam’iyyar PDP shi ne zaman lafiyar da ake samu a jihar Zamfara a lokacin mulkin Matawalle bayan tsawon lokaci ana fama da matsalar tsaro. Da yake nasa jawabin, Matawalle ya bayyana cewa ‘yan siyasa sun yanke hukuncin daya kamata da suka shigowa jam’iyyar PDP, kuma ya basu tabbacin ba zai nuna bambanci tsakanin su da tsofaffin ‘ya‘yan jam’iyyar ba.
You must log in to post a comment.