Home Labaru Matawalle Na Da ’Yancin Neman A Binciki Fadar Shugaban Kasa – Gwamnati

Matawalle Na Da ’Yancin Neman A Binciki Fadar Shugaban Kasa – Gwamnati

92
0

Gwamnatin Tarayya, ta ce Gwamna Matawalle na Jihar
Zamfara ya na da ’yancin fadin albarkacin bakin sa, na
bukatar Hukumar EFCC ta fadada bincike a kan jami’an da ke
cin rashawa zuwa Fadar Shugaban Kasa da ministoci masu
barin gado.

Gwamna Matawalle dai ya bukaci Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa, ya daina takura wa gwamnoni da bincike ya waiwayi fadar Shugaban kasa da ’yan Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Matawalle, ya bukaci shugaban hukumar EFCC ya tabbatar da cewa binciken hukumar ya zama cikakke ba tare da nuna wariya ba.

Sai dai Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu Lai Mohammed, ya ce gwamnan ya bayyana ra’ayin sa ne n kashin kansa, domin ya na da ‘yancin bada shawarwari.

Leave a Reply