Home Labaru Kasuwanci Matatar Dangote Za Ta Samar Da Guraben Aiki Ga Matasan Nijeriya 100,000

Matatar Dangote Za Ta Samar Da Guraben Aiki Ga Matasan Nijeriya 100,000

113
0

Sahararraen dan kasuwa Dangote Aliko Dangote, ya ce
sabuwar matatar man da ya bude za ta rika samar da ganga
dubu 650 a kowace rana, lamarin da ya ce zai samar da
guraben aiki ga matasa ‘yan Nijeriya akalla dubu 100.

Aliko Dangote, ya ce matatar za ta samar da akalla Dala biliyan 21 a kowace rana, lamarin da zai kawo karshen asarar makudan kudaden da Nijeriya ke kashewa domin shigo da mai daga kasashen ketare, ya na mai cewa yanzu haka kamfanin ya na da ma’aikatan da yawan su ya kai dubu 300.

Ya ce kaddamar da matatar man tamkar sharar fage ne na tabbatar da ana samar da isasshen mai cikin gida a kuma rika fitar da shi zuwa ketare, kamar yadda ya yi nasara a kasuwancin siminti da kuma takin zamani.

Aliko Dangote, ya ce karancin man fetur da ake fama da shi ya taba tattalin arzikin Nijeriya, lamarin da ya sa ya kudiri aniyar kafa katafariyar matatar man fetur domin kawo karshen wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, duk kuwa da tarin kalubalen ya ce ya fuskanta.

A karshe ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, za a rika fitar da kashi 40 cikin 100 na yawan man da ake hakowa a kowace rana.

Leave a Reply