Wani matashi mai suna Samson Sikiru, ya makare mahaifiyar
sa ta mutu har lahira a garin Ijebu Ode da ke jihar Ogun.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun Omotola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin.
Kanen wanda ake zargin ne ya sanar da makwaftan su abin da ke faruwa lokacin da ya dawo daga aikin gadi ya samu gawar mahaifiyar su a kwance.
Samson wanda ya kasance ba ya gida na tsawon shekaru, ya dawo ne domin yin bikin babbar Sallah tare da mahaifiyar sa makonni biyu da su ka gabata.
Rahotanni sun ce, an kama matashin ne bayan makwaftan su sun gano cewa shi ya kashe mahaifiyar sa, inda daga nan aka miƙa shi hannun ‘yan sanda.
Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun Omotola Odutola, ta ce matashin ya na fama da lalurar wakwalwa, domin a cewar ta, an kasance ana ɗaure shi lokuta da dama domin kada ya ji wa kan sa ko mutane ciwo.