Matar Ooni na Ife, Sarauniya Silekunola Moronke Naomi Ogunwusi ta sanar da rabuwa da mijinta, tareda sauka daga mukaminta na sarauniyar Ife.
Tsohuwar maid akin basaraken ta bayyana haka ne ta cikin wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta tabbatar da mutuwar auren da suka yi shekaru uku da suka gabata.
Naomi Ogunwusi ta kuma nuna godiya ga Allah bisa ni’imomin da ya yi mata cikin shekaru ukun da ta kwashe cikin matukar jin dadin inda tace Rayuwar duniya ba komai ba ce.
To sai dai tace mutuwar auren ta bashi da Alaka da sabon auren da Ooni ya yi a baya-bayan nan, Kamar yadda yawancin jama’a su za ku yi hasashe.
Ta kuma ce ba taba daukar ciki ba, baya ga dan da ta haifa mai suna Tadenikawo tana mai jaddada cewa tana da sakamakon binciken likita da zai tabbatar da cewa wannan haihuwar da ta yi, shi ne ciki na farko da ta taba dauka a duniya.