Home Labaru Maslaha:: Shugaba Buhari Ya Sa Ka Baki A Rikicin Sarkin Kano Da...

Maslaha:: Shugaba Buhari Ya Sa Ka Baki A Rikicin Sarkin Kano Da Gwamna Ganduje

589
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sa baki a rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

An dai dade ana kira ga Shugaba Buhari da dattawan arewa su sasanta tsakanin gwamnan da Sarki, duba da cewa rikicin ya na daukar sabon salo.

Wata amintaciyar majiya daga fadar shugaban kasa ta shaida wa manema labarai cewa, shugaba Buhari baya jin dadin abin da ke faruwa a jihar Kano, sakamakon korafe-korafe da fargabar tabarbarewar tsaro.

Ta ce Shugaba Muhammadu Buhari bai ji dadin yadda gwamnan ya rarraba masarautar Kano tare da yunkurin da ya ke yi na tsige sarkin ba, lamarin da ya sa ya ya kira Ganduje a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma umurci babban daraktan hukumar tsaro ta DSS ya kira taron gaugawa da gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma.

Shugaba Buhari ya kuma kira sarkin zuwa taron gaugawa tare da Madakin Kano Yusuf Nabahani.