Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da shirin sulhunta tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II.
Wutar rikici tsakanin Ganduje da Sarkin ta ta’azzara ne, tun bayan gwamnan ya kirkiri sabbin masarautu hudu, sannan ya daga likafar su zuwa masu daraja ta daya.
Wani kwamitin da ya samu goyon bayan shugaban kasa ya fara aikin sasanta shugabannin biyu a karkashin jagorancin Janar Abdulsalam Abubakar, kamar yadda sakataren kwamitin Adamu Fika ya bayyana.
Adamu Fika, ya ce sauran ‘yan kwamitin sun hada da Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya Kayode Fayemi, da Aminu Bello Masari da Janar Muhammadu Inuwa Wushishi da kuma Alhaji Abdullahi Ibrahim.
Sauran sun hada da Dakta Dalhatu Sarki Tafida da Dakta Umaru Mutallab da Farfesa Ibrahim Gambari da Sheikh Sharif Saleh.
Adamu Fika ya cigaba da cewa, kwamitin ya na aiki da sanin gwamnatin tarayya, kuma sun fara zama da shugabannin biyu, inda su ka nemi kowa ya maida wukar sa cikin kube.