Home Labaru Masarauta: Gwamnatin Kano Ta Sake Bijiro Da Batun Binciken Sarkin Kano

Masarauta: Gwamnatin Kano Ta Sake Bijiro Da Batun Binciken Sarkin Kano

376
0

Gwamnatin Jihar Kano ta sake bijiro da batun binciken zargin yadda aka kashe kudade wajen tafiyar da Masarautar Kano tun daga shekara ta 2013 har zuwa 2019.

Hukumar Karbar Koke da Hana Rashawa ta Jihar Kano ta aika wa Masarautar Kano wasika a ranar 2 Ga Mayu, inda ta nemi wasu jami’an kula da tasarifin kudaden fadar su bayyana a ofishin ta domin su yi karin bayani.

Wadanda aka gayyata dai sun hada da Babban Jami’in Kula da Harkokin Kudade Mohammed Kawu, da Shugaban Ma’aikata Mannir Sanusi, da Sakatare Isa Sanusi, da kuma Mujitaba Falakin Kano.

Takardar ta ce za su bayyana domin yin karin bayani a wasu wuraren da hukumar ke ganin an kauce Dokar Sashe na 26, wadda ta kafa Majalisar Masarautar Kano.

Leave a Reply