Home Labaru Martani: Talakawan Nijeriya Kadai Ke Son Gani Na A Kujerar Mulki –...

Martani: Talakawan Nijeriya Kadai Ke Son Gani Na A Kujerar Mulki – Buhari

214
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce tun farko manyan ‘yan Nijeriya ba su taba goyon bayan kudirin sa na siyasa wajen kasancewa shugaban kasa ba.

Sai dai ya ce a halin yanzu, ya zama dole manyan Nijeriya su yi godiya ga talakawan da su ka yi tsayuwar daka tare da jajircewa wajen tabbatar da kasancewar sa shugaban da zai tsamo Nijeriya daga kangin gazawa ta fuskar jagoranci.

Shugaba Buhari, ya ce manyan Nijeriya ba za su gushe wajen ganin bayan duk wani mai neman kujerar mulki da ke da manufar da ta saba wa burin su na siyasa da tattalin arziki ba.

Ya ce tarin dukiyar manyan Nijeriya ba ta yi tasiri wajen hana talakawa tabbatar da shi a matsayin shugaban kasa ba.

Buhari ya cigaba da cewa, domin neman amincewar talakan Nijeriya, babu karamar hukumar da bai ratsa ba tsakanin shekara shekara ta 2003 da sunan yakin neman zabe ba.