Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karyata zargin ba dan jam’iyyar APC kwangilar kayayyakin zaben Shugaban kasa da ya gudana a watan Fabrairu na shekara ta 2019.
A cikin korafin da su ka shigar a kotun sauraren kararrakin zaben Shugaban kasa, jam’iyyar PDP da Atiku Abubaka, sun yi ikirarin cewa an yi magudi a zaben, inda su ka ce an ba kamfanin Activate Technology Limited mallakar Alhaji Mohammed Musa kwangilar buga katunan zabe, wanda dan takarar kujerar sanata ne a karkashin jam’iyyar APC a jihar Neja.
Da ya ke maida martani ta bakin jagoran tawagar lauyoyin sa, Shugaba Buhari ya ce Alhaji Mohammed ba dan jam’iyyar APC ba ne, ya na mai cewa kwangilar da aka ba kamfanin da su ke ikirari ba mutum guda ba ne da Alhaji Mohammed Musa.
Shugaban Buhari, ya ce an ba kamfanin kwangilar ne tun a shekara ta 2011, ba wai lokacin dage zaben Shugaban kasa kamar yadda aka yi kuskuren bayyana wa a karar ba.
Buhari ya kuma jadadda cewa, sabanin ikirarin jam’iyyar PDP, ba ya da wata alaka ta jini tsakanin shi da jami’ar hukumar zabe Amina Zakari.