Jam’iyyar PDP ya ce babu wani a zo a gani a jawaban da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar dimokradiyya.
Sakataren yada labarai labarai na jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya kara da cewa a maimakon shugaba Buhari ya maida hankali a kan abubuwan da ke damun al’ummar Nijeriya, sai ya buge da wani sabon salon na daban.
Jam’iyar PDP dai, ta ce jawabin shugaba Buhari na ranar Dimokuradiyya cike ya ke da zuzuta ayyukan da ba’a aikata ba.
PDP ta ce, Buhari baida abin fade ga al’umar Nijeriya a kan kashe-kashe da garkuwa da mutane da kuma ayyukan da ‘yan bindiga da ke yi a wasu sassan Nijeriya, shi ya sa ya buge da wani sabon salo.
Jam’iyar ta cigaba da cewa, zaben ranar 23 ga watan Fabrerun shekara ta 2019 cike ya ke da magudi, wanda hakan ya sa su ke kotu domin ganin cewa an ba su hakkin su.