Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Martani: NAFDAC Ta Karyata Rahoton Da Ke Cewa Jabun Magunguna Sun Karade Nijeriya

Shugabar hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa NAFDAC Moji Adeyeye, ta karyata rahotannin da ke cewa hukumar ta ce mafi yawan magungunan da ake saidawa a Nijeriya duk na jabu ne.

Idan ba a manta ba, a ranar 19 ga watan Afrilu, jaridar ‘Vangard’ ta wallafa labarin da ke cewa NAFDAC ta ce kashi 70 cikin 100 na magunguna a Nijeriya na jabu ne.

Hakan ya sa Adeyeye ta bukaci mutane, da ma’aikatan kiwon lafiya da masu ruwa da tsaki su yi watsi da wannan rahoto domin babu gaskiya a cikin shi.

Ta ce tun da ta hau kujerar shugabancin hukumar ta maida hankali wajen ganin an kauda jabun magunguna a Nijeriya.

Moji Adeyeye, ta ce a shekara ta 2005, hukumar NAFDAC tare da hadin gwiwar kungiyar lafiya ta duniya da kamfanin Pharmacopeia da ke kasar Amurka, sun gudanar da bincike a kan jabun magungunan da ke Nijeriya, inda su ka gano kashi 16 cikin 100 ne kawai na jabu.

Exit mobile version